Zaman Aure – Ali Jita

 

SONG: Zaman Aure
ARTISTE: Ali Jita

LYRICS

[Intro]
Kauna da dadi, So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
ko mata ke hakuri

[Chorus]
Kauna da dadi So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
Ko mata ke hakuri

[Verse 1]
Aure dadi ne da shi
Aure ni’ima ce da shi
Aure rahama ce da shi
Duk dan halak yana ji da shi

Da kayi zaka kara girma
Budi zai zo ma da dama
Idon jama’a ka kara kima
Matar ka komai zata yi ma
Har wani mai Gida zata ce ma
Soyayya nada dadi

[Chorus]
Kauna da dai, So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
Ko mata ke hakuri

[Verse 2]
Gidan aure kala kala ne
Wani kaga laifin miji ne
Sai ya dau zigar mutane
Wai matayen mu matsala ne

Hakkin ta baza ai kula da shi ba
Bai san ya lallashe ta ba
Ko yayi shawara da ita ba
Bai girmama tunaninta ba
Ba jin dadin zaman suke ba
Maza ba karamin sake kuke ba

[Chorus]
Kauna da dai, So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
Ko mata ke hakuri

[Verse 3]
Mata na so a damu da su
A dunga wasanni da su
Wataran ku fito unguwa da su
Da yawa saukin kai ne da su

In ci kwalliya, ka ce tayi kyau
In ce abini, ce yayi dadi
Ku yi wasa ko babu kuddi
Kai mata yadda zata ji dadi
Zaman Auren ku zai kara dadi
Babu fada kuma babu kunci

[Chorus]
Kauna da dai, So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
Ko mata ke hakuri

[Verse 4]
Mata ku ma, ban bar ku ba
Wasu ba su san hakkin miji ba
Ko kwalliya, bata yi mai ba
Girkin sa ma bata dafa ba

In ci kwalliya, fita zata yi
Ko tambayar sa ma bata yi
Wata ma shanye shi zata yi
Babu abun da ya isa yayi
Yana gani ya za yayi
ki san allah bazai barki ba

[Chorus]
Kauna da dai, So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
Ko mata ke hakuri

[Verse 5]
Wata ma bata san kimar miji ba
Don ba gaida shi take ba
A gidan ba son zaman take ba
Bata so zaman lafiya ba

Baya taba ta sai ya biya ta
Su ciniki, nawa zaya bata
Kai lamarin nan ya kazanta
Ta ki ta barshi ya kara mata
Domin bakin kishi gare ta
Ta gwammace yaje ya bi mata

[Chorus]
Kauna da dai, So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
Ko mata ke hakuri

[Instrumentals]

[Chorus]
Kauna da dai, So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
Ko mata ke hakuri

[Bridge]
Zama na aure yana da dadi
Zama na aure mai sa nishadi
Aure mai ni’ima da fadi
Ango amarya suna zumudi
Zama na shirri da babu kaudi
farin cikin angwaye amare
Ai ba kamr randa anka tare
In ‘yan biki sunka kai amare
Kowa ya watse abarku tare
Zaman ku in kuka so ye dore
Gida na aure kala-kala ne
Wadan su za sui wal-wala ne
Wadan su na yin sakace ne
Wadan su na tona sirrika ne
Wadan su na cin amana ta aure
Wayyo soyayya da dadi
Haka nan soyyya da daci

[Chorus]
Kauna da dai, So da dadi
Zaman aure ma nada dadi
Zaman aure hakuri ake
Maza ne ke hakuri da mata
Ko mata ke hakuri


Recommend a Song



    YOU MAY ALSO LIKE

    Advertisement


    BROWSE BY CATEGORY

    Processional

    Recessional

    Reception Entrance

    Couple First Dance

    Father and Daughter

    Mother and Son

    Cake Cutting

    Bouquet Toss

    Garter Removal

    Money Spraying

    Yoruba Wedding

    Igbo Wedding

    Hausa Wedding

    Proposal